1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sakataren wajen Amurka Blinken na ziyara a Saudi Arebiya

April 29, 2024

Mr Blinken zai gana da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na Turai, don tsara jadawalin sake gina yankin Zirin Gaza da yakin ya ragargaza

https://p.dw.com/p/4fHY1
Hoto: Evelyn Hockstein/REUTERS

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sauka a birnin Riyadh na Saudi Arebiya a Litninin din nan, domin fara wata tattaunawar cimma yarjejeniyar tsagaita a yakin Gaza, tare da kara shigar da kayan agaji yankin.

Karin bayani:Blinken na matsa wa Isra'ila lamba don tsagaita wuta a Gaza

Haka zalika Mr Blinken zai ziyarci Jordan da Isra'ila, a ziyararsa ta bakwai yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar rikicin a ranar 7 ga watan Oktoban bara, biyo bayan harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila da ya zama silar yakin na wannan karo.

Karin bayani:Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, ya isa Masar kan sake gina Falasdinu

A yayin ziyar ta Riyadh, Mr Blinken zai gana da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na Turai, don tsara jadawalin sake gina yankin Zirin Gaza da yakin ya ragargaza, tare da raba al'ummar da matsugunansu.

Masar da Qatar da kuma Amurka ne dai ke jagorantar samar da masalaha kan wannan rikici da ke tunkarar watanni bakwai da barkewarsa.